logo

HAUSA

Dole ne Japan ta dakatar da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku da bin wata hanya mafi dacewa

2023-08-23 15:48:08 CMG HAUSA

Daga MINA

 

Ran 22 ga wata, gwamnatin Japan ta sanar da cewa, za ta zubar da ruwan dagwalon nukiliyar da take ajiye da shi cikin teku, tun daga gobe Alhamis 24 ga wata. Ta yi biris da rashin jin dadin da jama’ar duniya ke nunawa kan hakan, inda ta sanya jama’ar duniya tunkarar asarar da matakin nata zai haifar.

Jami’ar Tsinghua ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, bisa gwajin da ta yi, idan wannan ruwa ya shiga teku, zai isa gabar tekun kasar Sin bayan kwanaki 240, yayin da zai isa gabar tekun arewacin nahiyar Amurka cikin kwanaki 1200. Bayan shekaru 10 kuma, zai shafi dukkanin fadin teku a duniya. Matakin da Japan ke dauka, ba zai nisanta ita kanta da bala’in ba.

A hakika dai, shirin zai kawowa sha’anin kamun kifi a kasar Japan kalubaloli da dama. Hukuma mai kula da kayayyakin gona, da gandun daji, da teku, ta ba da kididdiga ta shekarar 2022, cewa yawan albarkatun teku da ake samu sun yi kasa tun daga shekarar 1956.

Ban da wannan kuma, kasashe ko yankuna 12, sun yanke shawarar hana shigar da kayayyakin teku daga Fukushima na Japan. Idan gwamnatin Japan ta aikata wannan shiri, to ba shakka kasashen duniya za su kara kayyade shigar da albarkatun teku, da abincin dake da nasaba da hakan daga kasar Japan, lamarin da zai kawo illar ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Duniya gidan daukacin bil Adama ne, kuma tsaron teku, da nagartattun muhallinsa, na amfanar jama’a matuka. Shirin da Japan take bi, zai sanya dukkanin fadin duniya yin asara. Ana fatan gwamnatin Japan za ta dakatar da wannan shiri, wanda ba wanda zai ci gajiyarsa, ta kuma nemi wata hanya da ta dace, kada ’yan siyasar kasar sun kare moriyar kansu ta bangarensu kadai, ta sanya duniya cikin mawuyacin hali. (Mai zana da rubuta: MINA)