Mutuncin Japan ya zube a duniya saboda shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku
2023-08-23 10:05:30 CMG Hausa
Jiya Talata, gwamnatin kasar Japan ta sanar da fara aiwatar da shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku tun daga ranar 24 ga wata, ko da yake, bangarori daban daban cikin kasarta da kasashen waje suka nuna adawa kan shirin. Al’ummomin kasar Japan, kungiyoyin kasashen duniya, da kasashen dake kewayen tekun Pacific sun yi Allah wadai da batun da kakkausar harshe, inda suka bukaci gwamnatin kasar Japan da ta soke wannan kuduri. Gamayyar kasa da kasa na ganin cewa, batun zubar da ruwan dagwalon nukuliya cikin teku ya saba wa dokar kasa da kasa, kuma zai haddasa matsalolin da ba za a iya warware su ba.
Tun lokacin da kasar Japan ta gabatar da wannan shiri yau shekaru 2 da suka gabata, mutanen kasa da kasa suka nuna shakku da damuwa matuka kan ko shirin ya dace da doka ko a’a, ko kuma yana da tsaro ko a’a. Domin sassauta damuwar jama’a, gwamnatin kasar Japan da kamfanin wutar lantarki na Tokyo sun yi alkawari cewa, ba za su zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba, in babu amincewar bangarorin da abin ya shafa kan wannan batu. Amma, mutuncin gwamnatin kasar Japan ya zube sabo da ba ta cika alkawarinta ba.
Ba kawai gwamnatin kasar Japan ta yi karya ga al’ummunta ba, har ma ta yi karya ga gamayyar kasa da kasa cewar, wai shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba zai haifar da matsala ba. A dayan bangare, kasar Japan ta canja ma’anar ruwan dagwalon nukiliya zuwa ruwan tsabtacen nukiliya, domin boye illar da ruwan zai haifar wa al’ummun duk duniya. haka kuma, kasar Japan ta kashe kudade da yawa domin sayan “iznin amincewa” kan shirinta.
Kana, bisa dokar teku ta MDD, kasashen duniya suna da hakkin kiyaye muhallin teku, a matsayin daya daga kasashen da suka sa hannu kan dokar, ya kamata kasar Japan ta dauki alhakinta yadda ya kamata. Kuma, gamayyar kasa da kasa suna da ikon kare kansu bisa doka, da kuma neman diyya daga kasar Japan. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)