logo

HAUSA

Nuna Bambanci A Fannin Ba Da Ilmi Na Lahanta Makomar Amurka

2023-08-23 15:23:07 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, ma’aikatar ba da ilmi ta Amurka ta yi bincike kan jami’ar Harvard kan ko ta nuna bambancin launin fata ko a’a yayin daukar dalibai, kuma ko ta fi son daukar daliban da suke da alaka da mutanen da suka baiwa jami’ar kyautar kudi ko kuma suka kammala karatu a jami’ar. Kwamitin kungiyar lauyoyi mai kula da hakkin dan Adam na Boston da dai sauran kungiyoyinsu 3 sun ba da kididdiga cewa, wadannan mutane da jami’ar ke fi son dauka, kashi 70 cikin dari fararen fata ne, yiwuwar daukar su karatu jami’ar ta ninka sau 6 ko 7 bisa sauran mutane. Wannan ya shaida cewa, daliban da suke da alaka da mutane fararen fata da suka baiwa jami’ar kyautar kudi ko kuma mutanen da suka kammala karatu a jami’ar, sun fi samun saukin shiga jami’ar, abin bakin ciki shi ne ba jami’ar Harvard kadai take yin haka ba, yawancin jami’o’in Amurka ke da wannan manufa. Kowa na da hakkin samun ilmi a jami’a, wanda ya danganta da kokarin mutane, amma jami’o’i kamar Harvard suna nuna bambancin launin fata yayin daukar dalibai, matakin da ya keta hakkin wasu daliban dake kokarin neman ilmi musamman wasu da suka kasance masu karamin karfi.

Ana fatan Amurka ta yi adalci da daidaici a fannin ba da ilmi a jami’o’i, kada irin wannan bambanci ya lahanta makomar Amurka a bangarori daban-daban.(Mai zana da rubuta: MINA)