logo

HAUSA

’Yan Najeriya na ci gaba da bayyana kyakkyawan fatan kasancewar kasar cikin kungiyar BRICS

2023-08-23 09:38:24 CMG Hausa

Yayin da taron shugabannin kungiyar kasashen BRICS ke gudana a kasar Afrika ta Kudu, masana tattalin arziki da na diplomasiyya a Najeriya na nuna shaukin kasancewar kasar cikin kungiyar ta BRICS.

A zantawarsa da wakilinmu dake Najeriya Garba Abdullahi Bagwai, wani masanin tattalin arziki, kuma babban malami a sashen nazarin harkokin tattalin arziki a jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce, shigar Najeriya cikin kungiyar shi ne mafita ga matsalolin tattalin arzikin da kasar ta shiga sakamakon bashin da kasashen yammacin Turai suka sanya ta a ciki. 

Yanzu ga ra’ayin Farfesa Garba Ibrahim Sheka da wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya hada mana daga Kano, Najeriya.

“A gaskiya wannan kungiyar ta BRICS kungiya ce da aka kafa ta domin bukasa tattalin arziki kuma China tana cikinta, kuma da gaske take nata agazawa kasashe kanana wadanda suke ciki, kamar yadda aka sani China da Rasha su suka hadu, Rasha ce ta assasa abun China kuma ta goyi baya, kasar Brazil ta shigo sannan Indiya ta shigo sai mu a nan kuma Afrika ta kudu ta shigo, amma an sa ni kasar Indiya da ita ce kasa ta biyu a sayen man Najeriya , amma yanzu abun ya dan canja domin sabo da BRICS da take ciki yanzu duk man da take saya daga Rasha ne, to ka ga shigarmu ciki zai iya sawa Indiya ta sake dawo wa ta zama daya daga cikin manyan abokan cinikayyarmu a fagen sayen mai, shiga cikin wannan yarjejeniya ya fi a ce kai ka dai kake abun ka, saboda za a samu sauki ko rangwame na wasu sharudodi masu tsauri, ina ganin shigar na da fa’idar gaske.”