logo

HAUSA

Me Ya Sa Nijeriya Ke Neman Shiga Tsarin BRICS?

2023-08-23 16:43:28 CMG Hausa



Daga Abdulrazaq Yahuza

Yanzu haka ana gudanar da taron kolin kasashen kungiyar BRICS (Brazil, Russia, India, China and South Africa) karo na 15 wanda Afirka ta Kudu ke karbar bakuncinsa. A shekarar 2009 ce aka kafa hadin gwiwar BRIC (Brazil, Russia, India da China), daga bisani bayan shigar Afirka ta Kudu a watan Oktoban shekarar 2010 aka mayar da sunan ya zama BRICS.

’Yan Nijeriya da dama masu kishin ci gaban kasar, sun yi na’am da yadda kasar ta nuna sha’awar shiga hadin gwiwar BRICS tare da takwarorinta na sassan duniya su 40, kamar yadda Jakadan Afirka ta Kudu a hadin gwiwan na BRICS, Anil Sooklal ya ayyana wa manema labarai kwanan baya.

Tambayar da wasu ke yi ita ce, me ya sa Nijeriya ke neman shiga wannan hadin gwiwa na BRICS? Galibin amsar da masharhanta ke bayarwa ita ce, kasar tana neman mafita a kan yadda za ta samu sukunin bunkasa tattalin arzikinta da kuma saukaka yawan dogaron da ta yi da dalar Amurka.

Nijeriya na so ta ci gajiyar hadin gwiwar BRICS kamar takwararta ta Afirka ta Kudu da ta samu ci gaban kasuwanci da kawayenta da kashi 10 cikin 100 a tsakanin 2017 zuwa 2021. Sannan hada-hadar kasuwancinta da kasashen BRICS sun bunkasa daga kudin kasar Rand Biliyan 487 a shekarar 2017 zuwa Rand Biliyan 830 a shekarar 2022.

Haka nan shigarta hadin gwiwar, zai bude mata sabon babin ci gaba ta bangaren bincike da kirkire-kirkire, makamashi, kiwon lafiya da bangaren ilimi. Tuni, har Afirka ta Kudu ta ci gajiyar ayyukan bincike sama da 100 a karkashin BRICS.

Bayan haka, kasancewar an kiyasta kayan da kasashen na BRICS ke fitarwa za su kai kashi daya bisa uku na duniya nan da 2030, sannan su ne ke da kusan kashi 18 cikin 100 na cinikin duniya, da mallakar kashi 26 cikin 100 na fadin duniya da kuma kusan kashi 42 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, Nijeriya za ta samu karin masu zuba jari daga kasashen hadin gwiwar baya ga bunkasa fitar da kaya zuwa waje.

Har ila yau, bisa irin rawar da Nijeriya ta taka a Afirka tun fil’azal, kamar shiga gaba wajen taya Afirka ta Kudu yaki da wariyar launin fata, da kashe wutar yakin basasa a Liberiya da Saliyo da gudunmawarta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, shiga hadin gwiwar na BRICS zai kara ba ta damar samun fada a ji a duniya musamman kan shirye-shirye da tsare-tsare na kashin dankali da Turawan yamma ke amfani da su.

Tabbas, BRICS hadin gwiwa ne na kasashe masu muradin ’yantar da kansu daga tsarin rashin adalci na kasa da kasa, ita ma Nijeriya na so a dama da ita!