Sin: Bai kamata kasashen waje su matsa lamba kan batun Libya ba
2023-08-23 11:00:38 CMG Hausa
Jiya Talata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya ba da jawabi a taron tattaunawa kan batun kasar Libya na kwamitin sulhu na MDD, inda ya jaddada cewa, bai kamata kasashen waje su matsa lamba kan batun kasar Libya ba.
Dai Bing ya ce, matsalar kasar Libya ta shafi siyasa, da tarihi, da kalibu da dai sauran harkoki, kuma, yadda kasashen waje suka matsa wa kasar lamba da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar sun haddasa yanayin tashin hankali cikin kasar Libya. Kwanan baya, bangarori daban daban na kasar Libya da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da kungiyoyin yankin sun bukaci a girmama ’yancin kai da mulkin kai na kasar Libya wajen warware matsalar kasar. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su mutunta da kuma lura da bukatun bangarorin kasar Libya domin magance ci gaba da matsa wa kasar lamba da bai kamata ba.
Ya kuma kara da cewa, yanzu, muna cikin muhimmin lokacin aiwatar da yunkurin siyasa a kasar Libya, kasar Sin tana goyon bayan bangarori daban daban na kasar Libya da su yi shawarwari, domin cimma matsayi daya kan batutuwan da abin ya shafa, ta yadda za a ciyar da yunkurin siyasa gaba kamar yadda ake fata.
Bugu da kari, ya ce, rikice-rikicen da suka tashi a babban birnin kasar Libya wato Tripoli kwanan baya sun haddasa rasuwa da jikatar mutane da dama. Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin kasar Libya da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, domin kiyaye yanayin tsagaita bude wuta yadda ya kamata cikin kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)