logo

HAUSA

Shin Japan biris za ta yi da hakkin al’ummarta da na makwabtaka?

2023-08-22 17:11:28 CMG Hausa

Abun mamaki da takaici, duk da adawa daga kasashe makwabta har ma da al’ummar kasar da suke zaman mafiya muhimmanci ga kowane kuduri ko manufar gwamnati, har yanzu Japan tana kan bakanta, inda ta sanar a yau Talata cewa, za ta  fara zubar da dagwalon nukilya a cikin teku a ranar Alhamis.

Shin Japan ba ta damu da koke da korafin da al’ummarta ke yi ba ne? Al’ummar kasar da kungiyoyi da kamfanonin masunta, sun bayyana matukar adawa da kudurin gwamnatin kasar, amma da alama, al’ummarta ba sa gabanta, illa abun da ta sa a gaba, wanda ka iya illata al’ummar duniya, har ma da toshewa al’ummarta hanyoyinsu na samun kudin shiga.

Su ma al’ummar Koriya ta kudu ba a bar su a baya ba wajen yi zanga-zangar adawa da wannan mataki,  a matsayinsu na makwabta da suka fi fuskantar barazanar illar matakin Japan, amma gwamnatinsu ta ki goya musu baya. Shin mene ne amfani gwamnati idan ba za ta tsaya ta kare muradun jama’arta ba? Gwamnati ta al’umma ce, kuma gwamnatin da ta cika gwamnati, ita ce mai sanya al’ummarta gaban komai, wannan ma wani darasi da ya kamata Japan ta dauka daga kasa kamar Sin.

Ba al’ummomin wadannan kasashe ba kadai, kuma ba kasar Sin ce kadai take adawa da wannan mataki ba, akwai tarin masana kimiyya da masu rajin kare muhalli da ma tsibiran yankin Fasifik da sauransu, da suka gargadi Japan ta dakatar da kudurin nata, ta kara nazari bisa kimiyya kafin aiwatar da shi, amma sanarwar ta yau, ta nuna cewa Japan ba ta shirya daga kafa ba.

Illar da wannan mataki za ta haifar ga daukacin al’ummar duniya, ya shafe duk wani buri da Japan ke son cimmawa. Haka zalika, Amurka dake ingiza ta, ita ma ba za ta tsira daga mummunar illar da hakan zai haifar ba domin an san cewa, ruwa ba shi da iyaka.

Har yanzu lokaci bai korewa Japan na sauraron al’ummarta da sake nazari domin yin abun da ya dace ba. Kuma ya kamata ta san cewa, baya ga al’ummarta, makwabtanta na da hakki a kanta, kuma Amurka dake ingiza ta, ba za ta kawo mata dauki ba idan abubuwa suka lalace.  (Faeza Mustapha)