Sheriff Ghali Ibrahim: Tsarin BRICS na kokarin sauya halin mamayar da kasashen yamma suka yi wa duniya
2023-08-22 15:11:43 CMG Hausa
Yau Talata 22 ga watan Agusta, an kaddamar da ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 15 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Kana kwanan baya wato ranar 19 ga watan nan ne, aka bude taron dandalin tattaunawa na kafofin watsa labarai na kasashen BRICS karo na 6, a kasar Afirka ta Kudu, inda aka yi kira da a kara daga muryoyin kasashe masu tasowa. Kimanin wakilai 200 daga kafafen watsa labarai kusan 100, da cibiyoyin bincike da kungiyoyin kasa da kasa daga kasashe kusan 30 ne suka tattauna a bisa taken "BRICS da Afirka: Karfafa tattaunawar kafofin watsa labarai don samar da makomar bai daya ba tare da son zuciya ba."
Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, shahararren masanin dangantakar kasa da kasa da batutuwan duniya daga jami’ar Abuja ta tarayyar Najeriya, na daya daga cikin mahalarta taron. Kafin tashin sa zuwa kasar Afirka ta Kudu, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da shi, inda ya bayyana muhimmancin tsarin BRICS, da kyakkyawan fatan sa ga ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 15, wadda aka fara tun daga yau Talata 22 ga watan Agusta. (Murtala Zhang)