Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a tallafa wa wadanda ta’addanci ya rutsa da su
2023-08-22 10:34:32 CMG Hausa
A jiya Litinin ne sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wa wadanda ta’addancin ya rutsa da su da kuma yin amfani da kwarewarsu wajen samar da sauyi domin samun kyakkyawar makoma.
Guterres ya yi wannan kira ne a wani sakon da ya aike na bikin ranar tunawa da wadanda ta'addancin ya rutsa da su, wanda ya fada a ranar 21 ga watan Agusta.
Taken wannan ranar ta kasa da kasa na bana shi ne "Gado: Neman bege da gina makoma mai lumana."
"A wannan rana, muna girmama duk wadanda suka rasu ko suka jikkata ta hanyar hare-haren ta'addanci a duniya," in ji Guterres. "Muna godiya ga aikin ban mamaki na wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira da suka yanke shawarar yin amfani da kwarewarsu don kawo canji." (Yahaya Babs)