Chen Mengli da surfanin kabilar Li
2023-08-22 09:48:35 CMG Hausa
Tsaunin Wuzhishan dake lardin Hainan a kudancin kasar Sin, shi ne garin Chen Mengli, ‘yar kabilar Li. Bayan ta gama karatun jami’a, ta koma garinta, inda ta fara yayata da nazari da sayar da surfanin kabilar Li, a kokarin ganin mutane da dama sun kara fahimtar al’adu da fasahar surfanin kabilar Li.
A shekarar 2018 lardin na Hainan ya samu damar gina tashar ciniki cikin ‘yanci. Chen Mengli ta yi amfani da wannan dama, wajen sanya surfanin kabilar Li fara yin suna a fadin duniya.
Yanzu kamfanin Chen Mengli ya bunkasa sosai, tare da samar wa mazauna wurin karin guraben ayyukan yi, wadanda suka samu abin dogaro da kai a garinsu, a maimakon zuwa cin rani a sauran sassan kasar.
Yanzu a kasar Sin karin matasa kamar Chen Mengli suna bar manyan birane, da koma garuruwansu don fara sha’anin da suke sha’awa, bisa hadin gwiwa da jama’ar garuruwansu. (Tasallah Yuan)