logo

HAUSA

Japan za ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya ta Fukushima a teku daga ranar Alhamis

2023-08-22 13:51:17 CMG Hausa

Gwamnatin Japan ta sanar a yau Talata cewa ta yanke shawarar fara fitar da ruwan dagwalon nukiliya daga gurbataccen tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Diichi cikin teku a ranar Alhamis, ta ce yanayi ya ba da dama.

Duk da adawar da ake samu daga gida da waje, firaminista Fumio Kishida ya sanar da matakin mai cike da cece-kuce bayan wani taron ministoci da aka gudanar a safiyar Talata din nan.

Wakilan masana'antun masunta na kasar a ranar Litinin sun jaddada kin amincewarsu da shirin zuba ruwan dagwalon a teku a yayin ganawar Kishida da shugaban kungiyar masunta ta kasar Japan da fatan samun fahimtar juna.

Kimanin kashi 88.1 cikin 100 na mutanen da aka nemi ra’ayinsu, sun bayyana damuwarsu kan shirin gwamnatin na zuba ruwan dagwalon nukiliyar a cikin tekun, yayin da makin rashin amincewa da majalisar ministocin da Kishida ke jagoranta ya yi karuwar watanni takwas, a cewar wani sabon binciken jin ra'ayin jama'a da kamfanin dillancin labaran kasar ya gudanar. (Yahaya)