logo

HAUSA

AU ta dakatar da Nijar daga kungiyar har sai an dawo da kundin tsarin mulkin kasar

2023-08-22 19:53:50 CMG Hausa

 

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da jamhuriyar Nijar daga kungiyar, har sai an dawo da kundin tsarin mulkin kasar, biyo bayan juyin mulki na baya-bayan da sojoji suka yi a kasar.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar Talatar nan, ta bayyana cewa, kwamitin zaman lafiya da tsaro na hukumar ta AU ne ya yanke shawarar dakatar da jamhuriyar Nijar daga kungiyar, a yayin taronta na baya-bayan nan game da halin da ake ciki a kasar da ke yammacin Afirka.

Sanarwar ta kuma nanata yin tir da juyin mulkin da wani bangaren sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli a Nijar din, wanda ya yi sanadin hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum daga mukaminsa.

Ta kuma bukaci sojojin da su sanya muradun Nijar da al'ummarta a gaban komai, su kuma gaggauta komawa barikokinsu ba tare da gindaya wani sharadi ba, kana su mika mulki ga hukumomin farar hula kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijar din ya tanada. (Ibrahim)