Wata tawagar ECOWAS a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar ta kai ziyarar aiki ta sa’o’i 48 a birnin Yamai
2023-08-21 19:55:06 CMG Hausa
Wata tawagar gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO ta kai wata ziyarar aiki a birnin Yamai daga ranar Asabar 19 zuwa Lahadi 20 ga watan Augustan shekarar 2023 a kokarin da take na shiga tsakani domin daidaita rikicin siyasa a Nijar. Wannan ne karo na biyu da tawagar yammacin Afrika take zuwa birnin Yamai.
Daga birnin Yamai din wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wannan tawaga dake karkashin jagorancin tsohon shugaban tarayyar Najeriya Abdulsalami Abubakar ta samu babban tarbo a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Diori Hamani dake birnin Yamai daga faraministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine da kuma mambobin kwamitin soja na CNSP da kuma mambobin gwamnatin rikon kwarya. Ita dai wannan tawaga ta hada musamman ma da sarkin Sokoto Muhammadu Sa’adu Abubakar, daya daga cikin shugabannin addinan Najeriya da kuma Omar Alieu Touray, babban kwamishinan CEDEAO.
Tsohon shugaban Najeriya da tawagarsa sun samu ganawa da shugaban kwamitin soja na CNSP kuma shugaban kasa birgadiye janar Abdourahamane Tiani a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai. Har ila yau da kuma tattaunawa tare da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine a fadar faraminista dake birnin Yamai. Haka kuma, tawagar kungiyar CEDEAO din ta samu ganawa da tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a Nijar, kungiyar CEDEAO ta sanyawa kasar takunkumi. Wannan tawagar hukumar yammacin Afrika dai ta soma wani aikin shiga tsakani domin neman bakin zare tare da sabbin hukumomin kasar ta yadda za’a cimma hanyoyi da damammaki da za su taimakawa wajen sassauta ko janye wadannan takunkumi da aka kakkabawa wannan kasa washe garin wannan juyin mulki, a cewar shugaban wannan tawagar a gaban ’yan jarida.
Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.