logo

HAUSA

Abokin Kirki Ya Fi Mugun Ɗan’uwa

2023-08-21 16:51:24 CMG Hausa

Ƙasar Sin a matsayinta na abokiyar hulɗar diflomasiyya ta ASEAN na tsawon lokaci, ta goyi bayan kiraye-kirayen tabbatar da zaman lafiya da tuntuɓa na diflomasiyya tsakanin ƙasashen ASEAN, yayin da take maraba da sabbin fatan yin haɗin gwiwa tsakanin Sin da ƙasashen ASEAN.

Goyon bayan da ƙasar Sin ta ba da a kan lokaci wajen kammala ƙa'idar aiki a tekun kudancin ƙasar Sin (COC) na da matukar muhimmanci wajen samar da zaman lafiya a yankin. Kalaman Wang Yi, yayin ziyararsa a kasashe uku na ASEAN, Malaysia da Singapore da Cambodia a kwanan baya, sun daidaitu a kan ra’ayi guda na warware saɓanin dake tsakanin tekun ta hanyar tuntuɓar juna da diflomasiyya. Kutsawar da jiragen ruwan Philippines suka yi a baya-bayan nan a tekun Ren'ai Jiao yana ƙara ƙarfafa buƙatar ɓangarorin yankin su ba da fifiko kan yarjejeniyar da aka daɗe da kafawa kan daidaiton harkokin tekun, da kuma hana masu kawo ruɗani irinsu Amurka tayar da husuma da haifar da saɓani a tsakanin makwabtan yankin.  

A mataki na biyu, muhimmiyar tattaunawar da Wang ya yi da firaministan ƙasar Singapore Lee Hsien Loong ta aza muhimman ginshiki na zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki. Kasar Singapore ta jaddada goyon bayanta ga shigar da ƙasar Sin cikin yarjejeniyar haɗin gwiwar tattalin arziki ta dijital (DEPA) tare da nuna aniyarta ta koyo daga yunƙurin zamanintarwa irin ta Sin. Kazalika, ɓangarorin biyu za su ƙara saurin samun ci gaba ta hanyar muhimman ayyukan gwamnatocinsu a yankunan Suzhou, Tianjin da Chongqing na ƙasar Sin, yayin da suke ƙara ƙuzarin gudanar da ayyukan bikin cika shekaru 15 na Sino-Singapore Tianjin Eco-City.

Dangantakar dake tsakanin Sin da Singapore ta riga ta tayi ƙarƙo tun lokacin ziyarar Lee a Beijing a farkon wannan shekara, ta sauya zuwa "babban haɗin gwiwa mai kyakkyawar makoma" kuma ta haifar da turjiya mai ma'ana ga duk wani yunƙuri na kutse, da tsangwama da katsalandan. Wang ya shaida wa Lee a lokacin da suke musayar ra’ayi cewa, ci gaban ƙasar Sin shi ne ci gaban zaman lafiya, da inganta matakan daidaita al'amura, waɗanda za su samar da fa'ida da damammaki masu ɗorewa ga dukkan ƙasashen duniya, musamman ma ƙasashen da ke makwabtaka da su.

Gagarumin ci gabar ƙasar Sin ta taimakawa "damammakin kasuwanci" da ƙarin jarin Sinawa a Malaysiya tare da samun ci gaba mai ɗorewa a karkashin manyan ayyukan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” irin su aikin laying dogo na East Coast Rail Link (ECRL), da sauransu.

Bayan haka, Beijing ya ci gaba da kasancewa babbar abokiyar cinikayyar Malaysia har tsawon shekaru 14, wanda hakan ya sa ya zama wajibi ga ɓangarorin biyu su faɗaɗa abin da Anwar ya bayyana a matsayin dangantakar abokantaka ta musamman "tare da tsayayyen" haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Firaministan Malaysia ya ce, "ƙasarsa na maraba da kamfanonin ƙasar Sin waɗanda za su faɗaɗa zuba jari a Malaysia, kuma Malaysia a shirye take ta zurfafa haɗin gwiwa da ƙasar Sin a fannoni daban daban domin cin moriyar juna da samun nasara tare." Yunƙurin da aka yi na inganta yawan kasuwancin ƙasashen biyu da ya kai dala biliyan 203.6 a bara shi ma wani babban ci gaba ne.

Ziyarar ta Wang a Cambodia ta zo daidai da cika shekaru 65 da kulla hulɗar diflomasiyya tsakanin Sin da Cambodia. Manyan ayyuka da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu suna nuni da ci gaban BRI ba tare da cikas ba, idan aka yi la'akari da yadda Cambodia ta himmatu da haɓaka ayyukan ci gaban ababen more rayuwa, makamashi, da ayyukan noma ga jama'arta.

Ƙasar Sin ta nuna matukar amincewa da tsarin da Cambodia ke bi wajen samun bunƙasuwa cikin sauri da kuma yawan jarin waje da aka samu a baya-bayan nan. Alamomin sakamakon da amincewar diflomasiyya na iya nuni da sabbin damammakin kasuwanci, kamar fahimtar farko tsakanin bangarorin biyu don ciyar da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta Sin da Cambodia (FTA) gaba.

A matsayinta na babbar abokiyar cinikayya ta Cambodia, kuma muhimmin tushen zuba jari da yawon bude ido, Beijing ta himmatu wajen inganta hulɗar dangantaka ta hanyar daidaita hanyoyin tattaunawa, da taimakawa zurfafa haɗin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare.  

Alkawuran da ƙasashen Sin da na ASEAN suka yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasa yankunansu na ci gaba da ɗaukar muhimman matsayi. (Yahaya)