logo

HAUSA

CMG da kafofin watsa labaran Afirka sun kulla sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa

2023-08-21 13:48:45 CMG Hausa

Babban rukunin rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice da manyan kafofin watsa labarai na kasashen Afirka da dama, wadanda suka hada da kawancen rediyon kasashen Afirka da kamfanin rediyo na kasar Afirka ta Kudu sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a jiya Lahadi 20 ga wata, a gabannin ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a kasar, inda kuma zai halarci ganawar shugabannin kasashen mambobin kungiyar BRICS karo na 15.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ANC kuma mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Paul Mashatile ya gabatar da wani jawabi a rubuce, inda yake fatan sassan biyu wato CMG da kafofin watsa labarai na kasashen Afirka za su samu babban sakamako yayin gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A nasa bangare, mataimakin shugaban ma’aikatar yada manufofin JKS kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, CMG da kafofin watsa labarai na kasashen Afirka za su yi hadin gwiwa na sabon zagaye, domin zurfafa zumuncin dake tsakaninsu, da kuma kafa makoma mai kyau a nan gaba. (Jamila)