logo

HAUSA

Teba yana kara sanya mutane fuskantar hadarin tsayawar bugun zuciya

2023-08-21 15:44:46 CMG Hausa

 

Karuwar teba, ba kawai alama ce ta karuwar nauyin jikin dan Adam ba, har ma masu nazari da suka fito daga kasar Birtaniya sun gano cewa, kara yin teba, yana kara sanya mutane fuskantar hadarin tsayawar bugun zuciya wato Heart failure a Turance.

To, mene ne ma’anar tsayawar bugun zuciya? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, wannan na nufin yadda jijiyoyin zuciya suke kasa aiki yadda ya kamata, ta yadda ba su da isasshen karfi, ta haka babu isasshen iskar Oxygen a cikin jinin da ya fito daga zuciya, lamarin dake da illa ga jikin dan Adam. Wadanda suke fama da wannan ciwo su kan ji gajiya da ko kuma kasa yin numfashi yadda ya kamata.

Jaridar The Times ta Birtaniya ta ruwaito cewa, masu nazari daga jami’ar Oxford sun tantance alakar da ke tsakanin gwajin kunkumi na baligai kusan dubu 430 ‘yan shekaru 40 zuwa 70 da haihuwa, da kuma lafiyar zuciyarsu cikin shekaru 13. Inda suka gano cewa, idan yayin gwajin kunkumin ya karu da centimita 1, to, hadarin da wadannan mutane suke fuskanta na kwantawa a asibiti sakamakon tsayawar bugun zuciya, ya karu da kaso 4. A ganin masu nazarin, a lokacin gwajin kunkumin dan Adam a nan ake fi gano ko akwai yiwuwar hadarin kamuwa da ciwon zuciya sakamakon matsalar kiba, gwargwadon mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum.

Masu nazarin sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a yayin da suka halarci taron hadaddiyar kungiyar kula da masu fama da ciwon zuciya ta Turai a kasar Spain. Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, mizanin BMI, wata alama ce da ke nuna ko mace ko namiji yana da kiba ko kuma babu. Amma gwajin kunkumi ya nuna mana yawan kibar da ke akwai a sashen tsakiyar jikin dan Adam, wanda yake da matukar muhimmanci a fannonin kibar da ke akwai a kuma hadarin kamuwa da cututtukan da ke shafar jijiyoyin zuciya.

Masu nazarin sun kara da cewa, kibar da ke akwai tana kewayen muhimman kayayyakin ciki, wadda ke haddasa cututtukan da ke shafar jijiyoyin zuciya.

Yanzu haka hukumomin lafiyar Birtaniya sun shawarci al’ummarta da su tabbatar da cewa, yanayin girman kunkuminsu bai kai rabin tsayinsu ba. (Tasallah Yuan)