logo

HAUSA

Jajircewa da azama! Farau da aka sadaukar don ceton rayuka a lokutan ba da agaji na gaggawa

2023-08-21 15:12:25 CMG Hausa


Song Yin jagaba ce, wadda Kyaftin ce ta kungiyar farko ta jiragen sama masu ayyukan ceto ta Donghai, a karkashin ma'aikatar sufuri ta kasar Sin. Kana tana daya daga cikin kyaftin mata na farko matuƙan jirgin sama mai saukar ungulu na aikin bincike da ceto a kasar. Tuni Song ta tabbatar da cancantarta, bisa yadda ta kashe sa'o'i sama da 3,395 wajen tukin jirgin sama, ciki har da sa'o'i 1,085 na tukin jirgi don aikin ceto, a cikin shekaru 15 da suka gabata. Bugu da kari kuma, a wannan lokacin, Song ta gudanar da ayyukan ceto 318, kuma ta taimaka wajen ceto mutane 225 a teku. Domin jajircewarta da azama, ake kiran ta da "Kyaftin Mace Mafi Kyau A Kasar Sin".

Song ita ce 'yar asalin birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, ta yi mafarkin tuka jirgin sama tun tana karama. A shekarar 2004, an shigar da ita Kwalejin hada-hadar teku wato Merchant Marine College ta Jami'ar koyan ayyukan teku ta Shanghai, wato Shanghai Maritime University.

A karshen shekarar 2007, jami’an ma’aikatar sufuri sun ziyarci jami’ar, domin daukar mata da za su zama matukan jirgin sama. Song ba ta yi jinkirin yin rajista don shiga cikin tsarin zabin ba.

Bayan kammala gwaje-gwaje masu tsauri da binciken lafiyar jiki, kana bayan zagaye da yawa a cikin tsarin zabin, an zabi Song don zama matukiyar jirgin sama ta kungiyar farko ta jiragen sama masu ayyukan ceto ta Donghai. Daga baya, ita da Wan Qiuwen, dayan macen da aka dauka, an tura su kasar Australiya don samun horon tuka jirgin sama da bincike da ceto har na tsawon watanni 15.

A shekarar 2010, Song da Wan sun ci jarrabawarsu ta karshe, kuma dukkansu sun sami lasisin tukin jirgin sama. Daga nan ne suka zama mata na farko matukan jirgin sama mai saukar ungulu dake aikin bincike da ceto a kasar Sin.

Mutane da yawa suna daukan tukin jirgin sama aiki ne mai dadi, amma tukin jirgin sama mai saukar ungulu dake aikin bincike da ceto abu ne mai wahala. Ganin yadda yanayi ke sauyawa a kai a kai da dalilan rikirkicewar yanayi a teku, aikin bincike da ceto, musamman a cikin teku, yana cike da kasada da hadari, kuma ba kawai kwarewar kwararrun ma'aikatan ceto yake bukata ba, har ma da hakuri da juriya.

Song ba ta taba tunanin dainawa ba, duk da wahalhalun da ta fuskanta. Ta samu dimbin kwarewar tuki da fasaha, kuma ta ci gaba da sha'awar sana'arta ta tashin jirgin sama.

Kullum yadda za ta ceto rayukan mutane ke gaban ta. Song ta bayyana cewa, "ta hanyar dawo da mutanen da suke bukatar ceto daga teku, hakika daidai yake da ceton iyalansu baki daya". Ta kara da cewa tana alfahari da kasancewarta matukiyar jirgin sama.

Song ta gudanar da ayyukan ceto da yawa, don haka ta fuskanci yanayi daban-daban masu hadari a lokacin aikinta na gomman shekaru.

Song ta gudanar da aikin ceto na farko a watan Nuwamba na shekarar 2010. Ita da tawagarta an ba su aikin ceto wani masunci, wanda ya karye a kafarsa yayin da yake aiki a wani jirgin ruwan kamun kifi. Ruwa na wucewa da jirgin, yayin da iska da igiyar ruwa ke bugun jirgin.

Song ta kasance cikin natsuwa, ta bincika bayanan da suka dace, ta kuma zura ido sosai kan halin da ake ciki a teku. A karshe, ita da abokan aikinta sun ceto mutumin da ya ji rauni cikin mintuna 10.

A karshen 2012, Song ta kammala wani aiki mai wahala. Ranar an yi dusar kankara, kuma sanyin ruwan teku ya kai kusan maki 0 a ma’aunin Celsius. Wani kwalekwalen kamun kifi ya mutu, ruwa na wucewa da shi.

Ma'aikatan jirgin 19 sun makale na tsawon sa'o'i 11 a lokacin da Song da tawagarta suka isa. Yawancin ma'aikatan jirgin sun gaji.

Ruwa na ta kada kwale-kwalen, kuma farfajiyar jirgin a jike ne da tsantsi, wanda hakan ya sanya ceton cikin hadari. Abu mafi muni shi ne, majanyar igiyar jirgin sama mai saukar ungulu ta makale yayin aikin ceton. Da kugiya ta kama wani kakkarfan abu a cikin kwale-kwalen ne, yadda ruwa ke girgiza kwale-kwalen da ya sanya jirgin sama mai saukar ungulun hadarin fadowa, watakila ma jirgin saman ta fada cikin teku. A cikin mawuyacin hali, Song ta zabi ta sake saita wajen sarrafa majanyar igiyar, cikin sa'a, majanyar ta fara aiki yadda ya kamata. Daga karshe dai an ceto dukkan ma'aikatan jirgin ruwan su 19.

A cikin 2015, an dagawa Song matsayi zuwa kyaftin, don jinjinawa gwanintarta da kwarewarta wajen iya tuka jirgin sama. Karin matsayin ya zo mata da karin nauyin da ke wuyanta. A watan Nuwamban wannan shekarar, wani kwale-kwalen kamun kifi ya kife, kan shi nutse a cikin ruwa. A matsayinta na kyaftin dake aiki a wannan rana, sako ya kai ga Song, daga cibiyar ceto na Donghai, sakon na cewa an samu wani dake raye ya makale a cikin jirgin ruwan, kuma ana bukatar a kai masu nutsewa cikin ruwa da kayayyakin nutsewa wurin da abin ya afku da jirage masu saukar ungulu. Song ta tuna da cewa, "a wannan aikin, mun tashi jirage biyar don jigilar dukkan kayan aikin nutsewa. Daga karshe ma'aikatan sun ceto wani mutum, wanda ya makale na tsawon sa'o'i 36 a cikin jirgin ruwan". 

Song ta kammala aikin ceton da ba a mantawa da shi ba a watan Disamban shekarar 2016. A ranar, wani kwale-kwalen kamun kifi ya kama wuta, kuma mutane 10 sun makale ciki. Yayin da Song da tawagarta ke tashi zuwa wajen jirgin ruwan, ta sami sabon bayani cewa, manyan igiyoyin ruwa sun tura kwale-kwalen gaba da mil 20 daga wurin da yake a da. 

Song ta duba wadatar man jirginta, sannan ta yanke shawarar tashi zuwa sabon wurin da kwale-kwalen yake. Asali, karancin man fetur aka tanada wa jirgin sama mai saukar ungulu, wanda hakan na nufin dole Song da tawagarta sun kammala ceto cikin kasa da lokaci fiye da yadda aka tsara a baya.

Tsananin yanayi, girman igiyar ruwa da hayakin dake tashi daga jirgin dake konewa ya sa aikin ceto ya yi wahala. Don hana hayakin yin tasiri a kan injunan jirgin sama mai saukar ungulu, dole ne jirgin saman ya yi shawagi a sama fiye da yadda aka saba. Song ta ci gaba da daidaita yanayin aikin jiragen saman don saukakawa mambobin tawagarta yin ayyukansu. A cikin rabin sa'a, an kwashe dukkanin masunta 10 cikin jirgin sama mai saukar ungulu. (Kande Gao)