logo

HAUSA

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta ce za ta kammala mika mulki a cikin shekaru uku

2023-08-20 15:52:51 CMG Hausa

 

Shugaban majalisar ceton kasa na jamhuriyar Nijar (CNSP) janar Abdourahamane Tchiani ya ba da shawarar komawa kan tsarin mulkin demokradiyya cikin shekaru uku.

Tchiani ya bayyana hakan ne, a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na kasa a yammacin jiya, inda ya ce gwamnatin mulkin sojan Nijar, za ta dauki matakai na gaggawa domin kawo karshen wannan matsala, tare da gayyatar dukkan sassan al'ummar kasar, da su tattauna tare da fito da muhimman ka'idoji da abubuwan da suka dace, wajen mika mulki cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Gwamnatin mulkin sojan Nijar za ta fara wata tattaunawa a fadin kasar, domin hada karfi da karfe kan dukkan sassa da nufin kafa ginshikin sabon tsarin mulki. Tchiani ya ce, majalisar CNSP na mutunta 'yancin jama'a na zabar gwamnatin da suke so.

Gidan talabijin na kasar Nijar ya bayar da rahoto a daren ranar Jumma'a cewa, kasashen Burkina Faso da Mali, sun aike da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu zuwa cikin kasar, domin mayar da martani kan duk wani nau'i na cin zarafi ga jamhuriyar Nijar daga kungiyar ECOWAS.(Ibrahim)