Yunkurin kasar Amurka na kafa wata kungiyar NATO a yankin Asiya da tekun Pasific ba zai yi nasara ba
2023-08-20 20:48:26 CMG Hausa
A jiya Asabar, an kammala wani taron shugabannin kasashen Amurka, da Japan, da Koriya ta Kudu, a Camp David na kasar Amurka, inda aka gabatar da wasu takardu don neman ruruta batun Taiwan, da na yankin tekun dake kudancin kasar Sin, da makamantansu, da ingiza kasashe daban daban su mayar da martani ga “barazanar”, gami da tsoma baki cikin harkokin gidan Sin.
Sai dai da wannan sakamako kasar Amurka za ta iya cimma burinta na kafa wata karamar kungiyar NATO a nahiyar Asiya? Hakika takardun da aka gabatar sun shafi yadda za a kafa tsari da musayar ra’ayi, da karfafa hadin gwiwa a fannonin tsaro, da tattalin arziki, da fasahohi. Wasu manazarta na ganin cewa, bisa la’akari da shirin kasashen Amurka, da Japan, da Koriya ta Kudu na gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa, takardun da aka gabatar tamkar wani alkawari ne da aka yi don biyan bukatun yakin neman zabe.
Ko da yake kasashen 3 sun yi ikirarin kulla huldar hadin kai a tsakaninsu, amma har yanzu suna da sabanin ra’ayoyi. Tun kafin bude taro na wannan karo, kasashen Amurka da Japan sun yi cece-kuce kan batun kama babban kifi na Whale. Kana kasar Japan, a nata bangare, ko da yake tana da burin zama wata “babbar kasa” a fannin aikin soja, amma duk da haka, za ta ci gaba da lura da alakarta da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki. Yayin da Koriya ta Kudu ke fuskantar matsala a fannin kula da huldar dake tsakaninta da kasar Japan, ko da yake ita ma tana da burin daga matsayinta a idanun duniya, ta hanyar kulla wani kawance tare da Amurka da Japan. Kana ba za a rasa sabanin ra’ayi ba tsakanin kasashen Amurka da Koriya ta Kudu, ganin yadda wasu dokokin da kasar Amurka ta gabatar dangane da kimiyya da fasaha, da hada-hadar kudi, ke haifar da mummunan tasiri kan wasu sana’o’in kasar Koriya ta Kudu, da take daukarsu da matukar muhimmanci.
Ta haka muna iya ganin cewa, kokarin kasar Amurka na neman kafa wata kungiyar NATO a yankin Asiya da tekun Pasific, ba zai taba yin nasara ba. (Bello Wang)