logo

HAUSA

’Yan Nijar mazauna Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna goyon baya ga kungiyar Ecowas

2023-08-20 14:42:41 CMG Hausa

 


A jiya Asabar 19 ga wata, wasu al’umomin Nijar mazauna Najeriya suka gudanar da wata zanga-zangar lumana ta nuna goyon baya ga kokarin kungiyar Ecowas na neman dawo da gwamnatin demkoradiyya a kasarsu.

Al’umomin dai sun gudanar da zanga-zangar ce a birnin Kano dake arewacin Najeriya inda suka koka ainun kan jinkirin sojin kasar na kin biyayya ga umarnin kungiyar Ecowas na maido da shugaba Mohamed Bazoum kan matsayinsa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.