Kasashen yamma ba su da aniyar ganawa da Rasha in ji Sergei Lavrov
2023-08-19 16:44:17 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya ce kasashen yammacin duniya ba su da sha’awar hawa teburin shawara tare da kasar sa, domin warware rikicin su da Ukraine.
Lavrov, wanda ya bayyana hakan a Asabar din nan, ya ce kasashen na yamma, sun gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki game da rikicin Rasha da Ukraine a birnin Jeddah, da Copenhagen, ba tare da gayyatar Rasha ba, kuma burin su shi ne janyo hankalin kasashen masu tasowa, ga shirin wanzar da zaman lafiya na shugaban kasar Ukraine.
Mista Lavrov, wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da mujallar “International Affairs”, ya kara da cewa, an yi watsi da muhimman burikan Moscow yayin da ake tattaunawa kan ricikin. Duk da cewa har kullum Rasha a shirye take ta shiga tattaunawar, ta kuma shafe shekaru tana neman Kiev ta aiwatar da yarjejeniyar Minsk, wadda ta tanadi warware rikicin dake addabar gabashin Ukraine.
Ya ce daga baya, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya soke duk wata tattaunawa da tsagin Rasha, ta amfani da dokar shugaba. A ganin mista Lavrov, masu samun goyon bayan kasashen yamma, na ci gaba da ingiza Ukraine, da nufin kara rura wutar yaki, kuma ga dukkanin alamu, a halin da ake ciki, babu yiwuwar komawa teburin shawara tsakanin Rasha da Ukraine, wadda kasashen yamma ke marawa baya.
Lavrov ya kara da cewa, Rasha na kallon kiraye-kirayen da kasashen yamma ke yi na a komawa tattaunawa, a matsayin wata dabarar samun lokaci, ta yadda dakarun Ukraine da suka riga suka gaji za su dan huta. (Saminu Alhassan)