logo

HAUSA

Faraministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da wata tawagar MDD dake karkashin Leonardo Simao

2023-08-19 14:49:52 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, wata tawagar MDD dake karkashin manzon musamman na MDD, kuma sakatare-janar na shiyyar yammacin Afrika da yankin Sahel, mista Leonardo Simao ta gana da faraministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine a ranar Juma’a 18 ga watan Augusta a fadar faraminista dake birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan ganawa tare da tawagar manzon musamman kuma wakilan sakatare-janar na MDD a shiyyar yammacin Afrika Leonardo Simao ta gudana a karkashin jagorancin faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine da mambobin kwamitin soja na CNSP musamman ma ministan tsaron kasa janar Salifou Mody da ministan cikin gida janar Mohamed Toumba.

Makasudin wannan ganawa tsakanin bangarorin biyu shi ne aza tubalin kaddamar da tattaunawa mai alfanu domin fita daga rikicin siyasa a Nijar.

Bayan wannan ganawa tare da faraministan rikon kwarya na Nijar, mista Leonardo Simao ya shaidawa manema labarai cewa,, wannan tattaunawa tare da faraminista da mambobin gwamnatinsa na cikin tsarin hulda tsakanin MDD da Nijar, ganawa da hukumomi masu fadi a ji, domin taimakawa kasar fita daga halin da ta shiga, ke nan dole da farko sai an saurari hukumomi, ra’ayoyinsu ta yadda za’a duba wannan matsala da ciwo kanta, domin kasa ta dawo cikin turbar demokaradiyya cikin lokaci mafi dacewa. Mun yi imani cewa kome na samun mafita tare da tattaunawa cikin halartar kowa, babu matsalar da ba za’a iyar magancewa idan ana tattaunawa, in ji manzon musamman na sakatare-janar na MDD.

Wakilin musamman na MDD kuma na sakatare-janar a shiyyar yammacin Afrika da yankin Sahel ya nuna cewa tare da tattaunawa, yana fatan za’a samu mafita cikin gaggawa domin warware wannan rikicin siyasa a Nijar. (Mamane Ada)