logo

HAUSA

Miliyan 2 VS miliyan 200

2023-08-18 22:00:33 CMG

Mutane sama da 100 suka jikkata, baya ga sama da dubu da suka bace, yayin da dubban gidaje suka lalace……Kwanan nan, gobarar daji da ta tashi a tsibirin Maui da ke jihar Hawaii ta kasar Amurka ta jawo hankalin duniya baki daya.

Gobarar dai ta kasance irinta mafi muni a Amurka cikin shekaru sama da 100 da suka wuce, gobarar ta haifar da munanan hasarori ga mazauna wurin, inda kwarya kwaryar alkaluman da aka samar suka shaida cewa, an fuskanci hasarar kimanin dala biliyan 6 ko ta fannin gidaje kawai. Da ake fuskantar wannan mummunan bala’i, gwamnatin Biden ta amince da samar da agajin da ya kai dala miliyan 2.3 ne kawai, a yayin ta sanar da samar da karin gudummawar soja da ta kai kimanin miliyan 200 ga kasar Ukraine.

Wannan mataki ya jawo suka daga al’ummar kasar, har ma wasu sun ce, “ko idan an sauya sunan Hawaii zuwa Ukraine, al’ummar da gobarar ta shafa za su samun karin gudummawa?”

Tsibirin Maui da a baya ya kasance mai kyakkyawan yanayi, amma ga yanayin da yake ciki yanzu. Ko su ci gaba da rura wutar rikici a duniya, ko kuma su mai da hankali a kan kashe gobara a gida, lallai, ya kamata ‘yan siyasar Amurka su yi tunani sosai a kai.(Mai zane:Mustapha Bulama)