logo

HAUSA

Wakilin Sin: Akwai bukatar yin shawarwari don shimfida zaman lafiya a Ukraine

2023-08-18 14:52:55 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron tattaunawa kan batun baiwa kasar Ukraine makamai cewa, akwai bukatar gudanar da shawarwari domin shimfida zaman lafiya a kasar Ukraine.

Jami’in wanda ya yi tsokacin a Jiya Alhamis, ya ce sau da dama, an tattauna kan batun baiwa kasar Ukraine makamai, kuma, kasar Sin ta sha jaddada matsayinta kan batun, kana, batun ci gaba da samar wa kasar Ukraine makamai ya yi matukar bata ran kasar Sin, kuma tana damuwa kan lamarin.

Geng ya kara da cewa, a halin yanzu, ana ci gaba da tura makamai masu dimbin yawa zuwa wuraren dauki ba dadi a kasar Ukraine, lamarin da ke yin tarnaki ga matakan da ake dauka na tsagaita bude wuta, da ma dakatar da musayar wuta baki daya a kasar ta Ukraine. (Maryam)