logo

HAUSA

Hukumar NAFDAC ta ja hankalin jama’a kan illar amfani da sinadarin sanya ’ya’yan itatuwa nuna da wuri

2023-08-18 09:17:02 CMG Hausa

Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna a tarayyar Najeriya NAFDAC ta gudanar da taron wayar da kan jama’a game da hatsarin amfani da sinadarin dake Sanya ’ya’yan itatuwa nuna da wuri “Calcium Carbide”.

Taron wanda aka gudanar da shi a garin Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya ya kunshi ’yan jaridu dake aiki a shiyyar da ’yan kasuwa, da masu rike da sarautar gargajiya da kuma wakilan kungiyoyi daban-daban.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

A yayin taron, hukumar ta NAFDAC ha’ila yau ta koka kan yadda ake samun karuwar masu sayar da magunguna barkatai a kasuwannin yankunan karkara a cikin kwanduna zafi rana na shafar su.

Taron wanda masana da dama suka yi dogon sharhi a kan yadda wasu ’yan kasuwa ke zuba sinadarin calcium carbide a cikin ’ya’yan itatuwa kamar Ayaba da Kankana da Mangwaro domin su nuna cikin sauri, inda aka bayyana hakan da cewa ta’addanci ne babba.

Da take jawabi shugabar hukumar ta NAFDAC a jihar Bauchi Madam Josephine Dylime ta bukaci ’yan jaridu da sauran jama’a da su baiwa hukumar hadin kan da ya kamata domin yakar wannan munmunar al’ada.

“Nunan ba zai yi har ciki sosai ba kuma nunan zai zama  jefi-jefi wani lokaci, kuma wani lokacin zai yi kyau sosai, amma kuma in ka ci kuma kana cin illa ne, zai kawo maka cuta a cikinka, shi ne muke son kowa ma ya ji wannan labari ta wurinku ’yan jaridu, za ku yada labarin da kuma wadanda suka zo daga kasuwanni da kungiyoyi wadanda za su taimake mu yada labaran nan, in suka ji zai gaya wa makwafta da yara da ba su samu ba, kowa zai samu labarin zai samu cin nasara a wannan yaki kuma zai sa mu samu tabbatar da lafiya a jikin mutane duka a Najeriya, shi ya sa aka ce NAFDAC safe guarding the Health of the Nation.”

Alhaji Murtala Malami shi ne ya wakilci hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta kasa Standard Organization Of Nigeria.

“Muna kira ka mutane, iyaye kan duk abun da za su saya ya zama akwai tambarin ranar da aka yi da ranar da wa’adin amfani da shi zai kare, sannan kuma akwai NAFDAC mamba da kuma tambarin inganci na SON idan ba ka same su ba to idan ka saya, kuma ka san wannan ra’ayin ka ne.”

A dai cikin rahoton da hukumar ta NAFDAC ta fitar a watan Yulin shekarar bara ya nuna cewa a kalla mutane 200,000 ne ke mutuwa a duk shekara a Najeriya sakamakon matsalolin gubar abinci wanda akasarin amfani da sinadarai barkatai ke haddasa hakan. (Garba Abdullahi Bagwai)