logo

HAUSA

Taron kolin BRICS zai ingiza daidaito da karsashi ga duniya mai cike da tashin tashina

2023-08-18 20:59:26 CMG

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce taron kolin kasashe mambobin kungiyar BRICS dake tafe, zai ba da damar zurfafa musaya game da manyan kalubalolin dake tunkarar sassan kasa da kasa a halin yanzu, da damar karfafa tsare tsare da hadin gwiwa a harkokin da suka shafi kasa da kasa. Kaza lika taron zai ingiza samuwar daidaito, da karsashi ga duniya mai fama da tashin tashina da sarkakiyar al’amura. 

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na yau Juma’a 18 ga wata, ya kara da cewa, taron na wannan karo zai gudana ne ido da ido, a karon farko cikin sama da shekaru 3, kana shi ne taron BRICS da a wannan lokaci zai sake gudana a nahiyar Afirka bayan shekaru 5.

Jami’in ya kara da cewa, dukkanin sassa mahalarta taron za su karfafa tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin BRICS da nahiyar Afirka baki daya, baya ga sauran kasashe masu tasowa. Har ila yau, taron zai gabatar da babbar murya, mai mara baya ga bunkasa cudanyar sassa daban daban, da mayar da hankali ga ci gaban bai daya. (Saminu Alhassan)