logo

HAUSA

An maida hankali ga hadin gwiwar fasahohin mutum-mutumin inji

2023-08-18 19:28:26 CMG Hausa

An kaddamar da baje kolin mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2023 a birnin Beijing a kwanan baya, burinsa shi ne baje kolin fasahohin zamani da sabbin nasarorin da aka cimma a fannin fasahar mutum-mutumin inji a duniya, da gina dandalin yin musayar fasahohi da hadin gwiwa da more nasara tare a wannan fanni.