logo

HAUSA

Kasar Sin na hada hannun kasa da kasa wajen inganta muhallin duniyarmu ta bai daya

2023-08-17 21:19:31 CRI

A kwanakin baya, kamfanin samar da motoci na kasar Sin da aka san shi da BYD, ya samar da mota mai aiki da lantarki ta miliyan 5, kuma hakan ya faru ne kasa da shekara guda, daga lokacin da ta samar da nau’in motar ta miliyan 3. A watan Yulin da ya gabata kuma, an samar da mota mai aiki da wutar lantarki ta miliyan 20 a kasar ta Sin.

Lallai bisa ga jagorancin gwamnatin kasar da ma tallafi da ta samar, kasar ta Sin ta samu gaggarumin ci gaba ta fannin samar da motoci masu aiki da lantarki, haka kuma ta zama kasuwa mafi girma a duniya ga nau’in motocin. Hakika, bunkasuwar motoci masu aiki da lantarki wani bangare ne daya kacal na ci gaban kasar Sin ta fannin kiyaye muhalli. A cikin shekaru 10 da suka wuce, kasa da kasa sun kuma shaida yadda kasar ta zama kasar da ta fi yawan karuwar dazuzzuka a duniya, kasar ta fi saurin inganta iskarta, baya ga yadda ta kasance kasar da ta fi yin tsimin makamashi da raya sabbin makamashi a duniya.

A kasance tare da mu cikin shirin Allah Daya Gari Bamban, don jin karin haske.