logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bayyana sabbin mambobin majalisar ministocinsa

2023-08-17 10:42:40 CMG Hausa

             

A jiya ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bayyana jerin sunayen ministocin gwamnatinsa, kimanin watanni uku bayan hawansa karagar mulki.

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale, bai shaidawa manema labarai ranar da za a rantsar da ministocin ba.

An nada Wale Edun, daya daga cikin manyan mashawartan Tinubu a matsayin ministan kudi. Sauran mambobin majalisar ministocin sun hada da Yusuf Tuggar, wanda aka nada a matsayin ministan harkokin waje, Mohammed Badaru Abubakar, ministan tsaro, yayin da aka nada Adegboyega Oyetola, a matsayin ministan sufuri.

Majalisar ministocin ta kuma hada da 'yan adawa, kamar yadda shugaban kasar ya yi alkawari na kafa gwamnatin hadin kan kasa da iya aiki.

Tun da farko dai, sai da majalisar dattawan Najeriya ta tantance sunayen ministocin kafin a nada su. (Ibrahim)