logo

HAUSA

Babban jami'in MINUSMA zai duba batun janye tawagar daga Mali

2023-08-17 10:33:35 CMG Hausa

Babban jami'in tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali (MINUSA), kana mataimakin babban sakataren MDD kan ayyukan samar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya nufi kasar Mali, domin ganawa da mahukuntan kasar kan shirin ficewar tawagar ta MINUSMA bisa tsari.

Mai magana da yawun MDD, Farhan Haq ya bayyana cewa, jami’in na MDD zai ziyarci Bamako, babban birnin kasar Mali, domin ganawa da mahukunta da masu ruwa da tsaki na kasar, domin tattaunawa kan ci gaban shirin janyewar dakarun tawagar sannu a hankali nan da ranar 31 ga watan Disamba.

Kakakin ya ce, ayarin motoci dauke da dakarun wanzar da zaman lafiya da kayan aiki daga sansaninsu na Ber da ke gabashin Timbuktu, sun isa birnin Timbuktu ranar Talata, a wani bangare na shirin janyewar. (Ibrahim Yaya)