logo

HAUSA

Shin Gobarar Da Ta Tashi A Maui Za Ta Iya Tada 'Yan Siyasar Amurka?

2023-08-17 21:33:02 CMG Hausa

Daruruwan mutane ne suka mutu, dubban mutane kuma sun bace, kana dubban gidaje sun lalace... Har zuwa yau Alhamis 17 ga wata bisa agogon wurin, ba a shawo kan gobarar da ta tashi a tsibirin Maui da ke jihar Hawaii ta Amurka ba.

A matsayinta na kasa mai karfin fada aji a duniya, Amurka ba ta da karancin kudi ko fasaha, amma ana sukar yadda take gudanar da ayyukan ceto. Tsarin gargadi na zamani ya gaza, kuma kungiyar ceto ta isa a makare, kana manyan sojojin Amurka ba su yi komai ba... Karancin ikon ba da agajin dakile bala'i na Amurka, ya nuna halin ko in kula da 'yan siyasa ke yi ga wahalhalun da jama'a ke sha.

Lokacin da wutar ta cinye tsibirin Maui, shi ma shugaban kasar Joseph Biden yana hutu. Lokacin da dan jarida ya tambaye shi game da asarar rayukan da aka yi a tsibirin Maui, ya yi murmushi tare da amsawa da cewa, “Babu wani sharhi,” wanda hakan ya jawo suka daga jama’a.

Har zuwa yanzu, gobarar dajin ta Maui tana ci gaba da yaduwa. Ba wai kawai ta kone gidajen Amurkawa da yawa ba ne, har ma ta "kone" abun da ke rufe gazawar 'yan siyasar kasar, tare da kara bayyana matsalolin tsarin gudanarwar Amurka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)