logo

HAUSA

Kamfanin jiragen sama na Delta zai kara yawan zirga-zirga tsakanin Amurka da Sin

2023-08-17 10:31:58 CMG Hausa

Kamfanin jiragen sama na Delta na Amurka, ya sanar da cewa, zai kara yawan zirga-zirga tsakanin Amurka da Sin, nan gaba a wannan shekara.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Laraba, ta ce daga ranar 29 ga watan Oktoba, kamfanin zai fara jigila a kullum daga birnin Seattle zuwa filin jirgin saman kasa da kasa na Pudong dake Shanghai, kana ya yi jigila sau uku a mako daga birnin Detroit.

Haka kuma, a watan Maris na badi, kamfanin zai dawo da zirga-zirga sau 4 a kowanne mako daga Los Angeles, hanyar da ta daina aiki tun cikin watan Fabrerun 2020.

A cewar shugaban kamfanin na yankin Asia da Fasifik Jeff Moomaw, yayin da ake samun karuwar bukata da shiga lokacin yawan tafiye-tafiye zuwa yankin Asia da Fasifik, kamfanin ya shirya maraba da karin matafiya zuwa yankin a lokacin hunturu dake tafe. (F a’iza Mustapha)