logo

HAUSA

Putin: Ana ci gaba da samun bunkasar tsarin daidaito tsakanin kasashe a duniya

2023-08-16 10:06:26 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin taron Moscow karo na 11 kan harkokin tsaron kasa da kasa cewa, ana samun bunkasar wani sabon tsarin daidaiton kasashe a duniya

A yayin da yake tattaunawa kan sauyin da duniya ke gani, wajen samun daidaito tsakanin kasashe, Putin ya ce, galibin kasashe a shirye suke su tabbatar da iko da kare muradun kasashensu, gami da al’adunsu

Shugaban na Rasha ya yi nuni da cewa, tsarin daidaiton kasashe a duniya, zai ba da gudummawa wajen samun ci gaba mai dorewa a duniya, da taimakawa wajen magance matsalolin zamantakewa, da tattalin arziki, da fasaha da kuma muhalli.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan tsaron kasar janar Li Shangfu ya halarci taron ya kuma gabatar da jawabi. (Ibrahim Yaya)