logo

HAUSA

Yadda Sin ke kokarin jawo jari da bunkasa cinikayya da kasashen Afirka

2023-08-16 09:25:07 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, majalisar gudanarwar Sin ta fitar wasu dokoki da suka shafi yadda za a kara jawo jarin waje da ma cin gajiyarsa yadda ya kamata. Dokokin sun bukaci da a inganta yanayin da ake cikin acikin gida da waje, da bunkasa yanayin kasuwar da babu kamarta a duniya, wanda kuma za ta dace da yanayi na kasuwaci, bisa doka da ka’idoji na kasa da kasa.

Ita ma hukumar dake tsara harkokin tattalin arzikin kasar Sin ta bayyana a yayin wani taro cewa, za ta himmatu wajen kara ci gaba da yin gyare-gyare, da nacewa kan ka'idar tabbatar da bunkasar tattalin arziki yadda ya kamata a matsayin babban fifiko, da neman ci gaba, yayin da ake tabbatar da daidaito.

A cewar taron, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare, wadda ke tsara tattalin arziki, ta bayyana ayyuka shida a wurin taron, wadanda suka hada da ka’idojin tafiyar da harkokin kudi, inganta amfani da kayayyaki da kara zuba jari, tallafawa ayyukan samar da kayayyaki da hidima, zurfafa gyare-gyare da bude kofa, karfafa ginshikin tsaron tattalin arziki, da tabbatar da kyautata jin dadin jama'a.

Bugu da kari taron ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da samar da damammaki, da kuzari, kuma tushen tattalin arzikin kasar na dogon lokaci bai canza ba.

A bangaren Sin da Afirka kuwa,Sin da Angola sun amince su tsara dabarun inganta hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, da kara habaka hadin gwiwar cinikayya da zuba jari, da karfafa nasarorin da aka cimma a hadin gwiwar samar da ababen more rayuwa, da fadada cudanya a fannonin makamashi, da ma'adinai, da masana'antu, da aikin gona, da kamun kifi.

Haka kuma jami’an Sin da Afirka ta kudu, sun yi musayar ra’ayi kan zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashensu, tare da share fagen taron shugabannin kungiyar BRICS karo na 15 a fannonin cinikayya da tattalin arziki. Wannan na kara nuna cewa, ‘yan kasuwar waje na kara nuna sha’awar shiga babbar kasuwar Sin mai cike da damammaki. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)