logo

HAUSA

MDD: Rikici a Sudan ya haifar da bala'o'in jin kai

2023-08-16 10:01:27 CMG Hausa

A jiya Talata ne hukumomin majalisar dinkin duniya suka bayyana cewa, watanni hudu da aka kwashe ana rikici a Sudan, ya haifar da bala’o’in jin kai da kuma take hakkin bil Adama. 

William Spindler, kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR, ya shaidawa manema labarai cewa, tun farkon rikicin a watan Afrilu, sama da mutane miliyan 4.3 ne suka yi hijira a dalilin tashin hankalin.

Margaret Harris, mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce rikicin ya yi illa ga rayuwar mutane, da kiwon lafiya da walwala. "Kusan kashi 67 cikin 100 na asibitoci ba su aiki a mafi yawan wuraren da abin ya shafa." A cewar ta.

Elizabeth Throssell, mai magana da yawun ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar OHCHR, ta ce ko da yake ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu a halin yanzu, alkaluma na nuni da cewa, ya zuwa yanzu an kashe sama da mutane 4,000 da suka hada da daruruwan farar hula. (Yahaya)