logo

HAUSA

Masar da Saudiyya sun yi kira ga Larabawa zalla da su magance matsalar shiyyar

2023-08-16 11:22:07 CMG HAUSA

 

A jiya ne, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry, ya gana da takwaransa na kasar Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan Al Saud a birnin Alkahiran Masar, inda suka bukaci hadin kan kasashen Larabawa, da kuma daukar matakai na hadin gwiwa don magance rikice-rikicen dake faruwa a kasashen Larabawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, taron ya tattauna hanyoyin inganta hanyoyin tuntubar juna da hadin gwiwa tsakanin Masar da Saudiyya kan batutuwan da suka shafi yankin, ciki har da rikice-rikice dake faruwa a kasashen Sudan, da Libya, da Yemen da kasar Syria.

Ministocin biyu sun jaddada wajibcin ciyar da tsare-tsaren hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa gaba, wajen tinkarar rikice-rikice daban daban dake faruwa a shiyyar ta hanyar shawarwarin "Larabawa zalla" domin kiyaye tsaron kasashen na Larabawa.

Manyan jami'an diflomasiyyar kasashen biyu sun kuma tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen ganin an warware rikicin Palasdinu da Isra'ila cikin adalci, wanda zai ba da tabbacin kaiwa ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta, bisa kudurorin da kasashen duniya suka cimma. (Ibrahim)