logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke hada hannun kasa da kasa wajen inganta muhallin duniyarmu ta bai daya

2023-08-15 22:36:37 CMG Hausa


Daga Lubabatu Lei

A kwanakin baya, kamfanin samar da motoci na kasar Sin da aka san shi da BYD, ya samar da mota mai aiki da lantarki ta miliyan 5, kuma hakan ya faru ne kasa da shekara guda daga lokacin da ta samar da nau’in motar ta miliyan 3. A watan Yulin da ya gabata kuma, an samar da mota mai aiki da wutar lantarki ta miliyan 20 a kasar ta Sin.

Lallai bisa ga jagorancin gwamnatin kasar da ma tallafi da ta samar, kasar ta Sin ta samu gaggarumin ci gaba ta fannin samar da motoci masu aiki da lantarki, haka kuma ta zama kasuwa mafi girma a duniya ga nau’in motoci. Idan an lura, za a ga karin motoci masu aiki da lantarki da ke wucewa a titunan sassa daban daban na kasar, baya ga kuma karin na’urorin da aka kafa domin yi wa motocin caji.

Hakika, bunkasuwar motoci masu aiki da lantarki wani bangare ne kawai na ci gaban kasar Sin ta fannin kiyaye muhalli. A cikin shekaru 10 da suka wuce, kasa da kasa sun kuma shaida yadda kasar ta zama kasar ta fi yawan karuwar dazuzzuka a duniya, da kasar ta fi saurin inganta iskarta, baya ga yadda ta kasance kasar da ta fi yin tsimin makamashi da raya sabbin makamashi a duniya. Duk wadannan sun faru ne sakamakon yadda manufar nan ta “kyakkyawan muhalli shi ne kadarori masu kima” ke kara zame wa Sinawa jini da tsoka a rayuwarsu ta yau da kullum, manufar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005, wanda a lokacin ya kasance sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen lardin Zhejiang da ke gabashin kasar. Sakamakon manufar, a cikin shekaru 18 da suka wuce, duniya ta shaida yadda kasar Sin ta yi ta kara kyaunta, haka kuma ta samar da gudummawar kasar Sin ga kyautata muhallin halittu na duniya baki daya.

In mun dauki sabbin makamashi a misali, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta zamanto ta farko a duniya ta fannin samar da sabbin makamashi, don haka ma, ya zama muhimmin bangaren kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.

A yankin De Aar da ke tsakiyar kasar Afirka ta kudu, fararen na’urorin samar da wutar lantarki da makamashin iska, suna samar da lantarki sama da KW miliyan 750 a kowace shekara, kuma ta hakan an yi tsimin kwal kimanin tan sama da dubu 200, tare da rage fitar da iskar Carbon kimanin tan dubu 700. Sai kuma a yankin Garrisa na kasar Kenya, kamfanin kasar Sin ya kafa tashar samar da lantarki da makamashin rana irinta mafi girma a gabashin Afirka, wanda ya sassauta matsalar karancin wutar lantarki da kasar ta fuskanta, amma kuma ba tare da fitar da iskar Carbon ba. A kasar Nijeriya kuma, kamfanin kera bas bas na Yutong na kasar Sin, ya samar da bas bas masu aiki da wutar lantarki a birnin Lagos, karon farko ke nan da kasar ta shigo da bas bas masu aiki da sabbin makamashi.

A kokarin da kasar Sin ke yi, an kaddamar da jerin shirye-shirye na tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a dimbin kasashe masu tasowa, wadanda suka sa kaimin kyautata muhallin halittun duniya.

Duniyarmu gida ne na bai daya ga dukkanin ‘yan Adam, kuma ‘yan Adam makomarsu daya ce a yayin da suke fuskantar matsalolin muhalli. A yayin da kasar Sin ke ci gaba da inganta muhallin halittu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da samar da gudummawarta, ta hada hannu da sassan kasa da kasa, musamman ma kasashen Afirka, don kara inganta muhallin duniyarmu ta bai daya. (Lubabatu Lei)