logo

HAUSA

Jirgin NAF Ya Yi Hatsari A Neja

2023-08-15 11:16:56 CMG HAUSA

Bisa labarin da jaridar Leadership ta Najeriya ta bayar an ce, wani jirgi mai saukar ungulu na dakarun mayakan sojan saman Nijeriya (NAF) ya gamu da hatsari a kauyen Chukuba da ke cikin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a ranar Litinin.

Jirgin wanda ya yi hatsarin a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga jihar Neja yayin da ke sintirin kwaso wadanda aka jikkata.

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

Sai dai babu wani bayanin da ke nuna akwai wadanda suka jikkata ko kuma wadanda suka tsira a hatsarin a zuwa lokacin hada wannan rahoton yayin da NAF ta ce ta na kan kokarin ceto wadanda suke cikin jirgin a lokacin da ta yi hatsari.