Sani Tajo Kunya: Ina fatan yin amfani da ilimin da na samu a kasar Sin don taimakawa harkokin noma a Najeriya
2023-08-15 15:06:47 CMG Hausa
Sani Tajo Kunya, dalibi ne dan asalin Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a cibiyar nazarin kimiyyar aikin noma ta kasar Sin wato Chinese Academy of Agricultural Sciences a turance. A halin yanzu yana gudanar da wani bincike a birnin Anyang na lardin Henan na kasar ta Sin.
A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Sani ya bayyana ra’ayinsa kan rayuwa da yake yi a kasar Sin, da bambancin yanayin karatu dake akwai tsakanin Najeriya da Sin, da yadda zai yi amfani da ilimin da ya samu a kasar, don taimakawa ga ci gaban sana’ar noma a kasarsa wato Najeriya. (Murtala Zhang)