logo

HAUSA

Hadin gwiwar CMG da kafafen yada labarai na Afrika zai fahimtar da al’umma kyakkyawar aniyar kasar Sin

2023-08-15 19:10:14 CMG Hausa

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da kungiyar kawancen gidajen rediyo ta Afrika, sun gudanar da taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwarsu, jiya Litinin a Nairobin kasar Kenya.

Muhimmancin kafofin watsa labarai a tsakanin al’umma abu ne mara misaltuwa, kasancewarsu tamkar gada tsakanin al’umma da wajen yankunansu. Kafar watsa labarai tamkar makaranta ce dake kan ilmantar da al’umma.

Hadin gwiwar CMG da kafafen yada labarai a nahiyar Afrika, musamman a irin wannan lokaci da karairaiyi da zarge-zarge suka kara yawa, zai taka gagarumar rawa wajen ilmantar da al’ummun nahiyar Afrika game da yanayin kasar Sin da kyakkaywar aniyarta gare su, har ma da dimbin tallafi da goyon baya da take ba nahiyar, haka kuma zai kara fahimtar da Sinawa ainihin yanayin da nahiyar Afrika ke ciki.

Rashin fahimta tamkar wata cuta ce dake bukatar kulawar likita. Yadda kafafen yada labarai na yammacin duniya suka yi kaka-gida a kasashenmu na Afrika, ya sa suke yada jita-jita  da zummar haddasa fitina da shafawa Sin bakin fenti, domin cimma muradun kasashensu na babakere da dakile karbuwar kasar Sin a nahiyar.

Kyautatuwar alaka ko aminci mai karfi tsakanin Sin da kasashen Afrika, ya sa kafafen yada labarai na yammacin duniya ke kara wasa wukarsu na shafawa kasar Sin bakin fenti. Wannan ya sa nake ganin alaka ko kawance tsakanin kafafen yada labarai na Sin da Afrika ke da muhimmanci gaya, domin bangarorin biyu za su bayar da hakikanin labarai bisa yanayi na gaskiya da adalci ta yadda al’umma za su iya gane ainihin yanayin da duniya take ciki da ma wadanda ba sa son ganin ci gabansu.

kamar yadda hadin gwiwar Sin da Afrika ke haifar da kyawawan sakamako a sauran fannoni, haka hadin gwiwa tsakanin CMG da kafafen yada labarai na Afrika zai yi kyakkyawan tasiri wajen fahimtar da al’umma game da irin kyakkaywar alakar dake tsakanin Sin da Afrika, domin su fahimci cewa, kasar Sin aminiya ce ta kwarai. Kana zai kai ga samun goyon bayan juna mai dorewa tsakanin al’ummomin, har ma da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya. Bugu da kuma kari, zai dakile yunkurin masu kokarin lalata wannan kyakkyawar dangataka. (Fa’iza Mustapha)