logo

HAUSA

Kamfanin samar da wutar lantarki na Hawaii na fuskantar shari'a dangane da mummunar gobarar daji ta Maui

2023-08-15 10:26:19 CMG Hausa

A yayin da adadin wadanda suka mutu sanadiyar gobarar dajin da ta tashi a tsibirin Maui na jihar Hawaii na kasar Amurka ya karu zuwa 96, ya zuwa jiya, an shigar da babban kamfanin samar da wutar lantarki na jihar kara a gaban kotu dangane da bala’in.

A ranar Asabar ne aka shigar da kamfanin na Hawaiian Electric kara a gaban kotu, inda ake zargin layin samar da wutar kamfanin dake Maui da haddasa tashin gobarar daji mafi muni a tarihin Amurka na wannan zamani.

Wasu sabbin bayanai daga hukumar na cewa, ya zuwa jiya, gobarar ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 96 tare da lalata gine-gine sama da dubu biyu, baya ga mutanen da ba a san adadinsu ba da suka bace.

Ba a dai tantance musabbabin tashin gobarar ba, amma masu shigar da kara sun bayyana a cikin takardar karar mai shafuka 37 cewa, na'urorin kamfanin na iya zama silar tashin wutar. (Ibrahim Yaya)