logo

HAUSA

Za a kawo sauye-sauye a tsarin sufuri a jihar Adamawa

2023-08-15 09:47:15 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Adamawa dake arewa masu gabashin Najeriya ta tabbatar da cewa, tana nan tana kokarin kawo sabbin sauye-sauye a fagen sha’anin sufuri a manyan garuruwan jihar domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta tun bayan janye tallafin mai fetur.

Kwamishinan harkokin sufuri na jihar Alhaji Musa Mahmud Kallamu ne ya tabbatar da hakan jiya Litinin a birnin Yola, fadar gwamnatin jihar yayin taron manema labarai, ya ce batun sufuri na daya daga cikin muhimman ayyukan da gwamnati ke son baiwa fifiko a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Daga Tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Alhaji Musa Mahmud Kallamu ya ce, gwamnatin jihar za ta kara odar wasu sabbin motocin bus kari a kan wanda ake da su na ADAMAWA SUNSHINE da kuma kananan babura masu kafafuwa uku wadanda za su rinka daukar jama’a a kan farashin mai saukin gaske.

Alhaji Musa Mahmud wanda ya kara da cewa, jihar Adamawa na amfana sosai ta fuskar kudaden shiga ta hannun ’yan kasuwa da suke safarar kayan amfanin gona daga yankunan daban-daban na jihar zuwa wasu sassan Najeriya da kuma jamhuriyyar Kamaru da suke makwaftaka da ita.

Ya ce, hakika gwamnatin jihar tana damuwa sosai daga irin halin matsin da al’ummar jihar suka shiga na tsadar sufuri musamman ma a wannan lokaci.

“Sako da za mu baiwa al’ummarmu shi ne jama’a su yi hakuri da wannan lokaci da muke a ciki, kuma gwamnati tana kokari domin ta kawo sauki ga jama’arta, kuma gwamna Amadu Fintiri ba a bar shi a baya ba a wannan harka, akwai abubuwa da yawa da aka samu a gefen sufuri wanda kuma ba sa yi wa jama’a dadi ba gwamnati kuma tana asara a ciki, wannan shi ne manufarmu kuma muna godiya ga Allah da kuma shi gwamna.” (Garba Abdullahi Bagwai)