logo

HAUSA

Shugabannin Masar, Jordan da Falasdinu sun bukaci kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi, da kuma farfado da tattaunawar zaman lafiya

2023-08-15 10:34:36 CMG Hausa

A jiya Litinin ne shugabannin kasashen Masar, Jordan da Falasdinu suka jadadda wajibcin kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinu domin farfado da zaman lafiya da ci gaban Falasdinawa, a cewar sanarwar da fadar shugaban Masar ta fitar.

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-sisi, Sarki Abdallah na biyu na Jordan da shugaban falasdinu Mahmoud Abbas sun gudanar da wani taro a birnin New Alamein dake gabar tekun Masar, inda shugabannin uku suka tabo batutuwan da suka shafi al'ummar Falasdinu.

Shugabannin sun jaddada bukatar al'ummar Falasdinu na samun dukkanin hakkokinsu, da suka hada da kafa kasa mai cin gashin kanta a bisa yarjejeniyar shekarar 1967 da gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta, da warware matsalar ’yan gudun hijira Falasdinawa bisa ga kudurin hakkin kasa da kasa. (Yahaya Babs)