logo

HAUSA

Ranar giwaye ta duniya

2023-08-15 11:24:41 CMG Hausa

Ranar 12 ga watan Agustan kowace shekara, ranar giwaye ce ta duniya. An ayyana ranar tun a shekara ta 2012.

Sauye-sauyen muhallin halittu sakamakon sauyin yanayi, da ayyukan farauta da zummar sace haurin giwa, da ya ki ci ya ki cinyewa, abubuwa ne dake kawo babbar barazana ga rayuwar giwaye a fadin duniya. Makasudin ayyana wannan rana, ita ce ilimantar da jama’a, da su kula da giwayen Afirka da na Asiya wadanda ke cikin kuncin rayuwa.