logo

HAUSA

Hanyar mota daga gabashi zuwa yammacin Aljeriya ta zama kyakkyawan misali ga hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”

2023-08-14 19:47:03 CMG Hausa

Kwanan nan ne aka kaddamar da wata babbar hanyar mota, wadda ta tashi daga gabashi zuwa yammacin kasar Aljeriya, wadda kamfanin kasar Sin ya shimfida. Hanya ce da ta samu babban yabo daga al’ummar wurin, kana kyakkyawan abun misali ce ga hadin-gwiwar Sin da Aljeriya, har ma da Sin da Afirka, a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa na fatan yin kokari tare da kasar Aljeriya, da ma sauran kasashe, wajen kara bunkasa shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za’a taimaka ga farfado da tattalin arziki, gami da ci gaban duniya mai dorewa.

Bugu da kari, a wajen taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, Wang ya kuma maida martani game da harin da aka kai wa wasu injiniyoyin kasar Sin dake tashar jiragen ruwa ta Gwadar a kasar Pakistan, yana mai cewa, kasar Sin na matukar Allah wadai da irin wannan harin ta’addanci, ta kuma bukaci Pakistan da ta yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata wannan ta’asa, tare kuma da daukar matakan da suka wajaba, don tabbatar da tsaron mutanen Sin dake wajen. (Murtala Zhang)