logo

HAUSA

Rikicin kabilanci ya yi sanadiyar kashe mutane kusan 50 a kudancin Sudan

2023-08-14 09:52:50 CMG HAUSA

 

Jaridar "Sudan Tribune" da ake wallafawa a kasar Sudan, ta bayyana cewa, rikicin kabilanci da ya barke a Nyala, babban birnin kudancin Darfur jiya Lahadi ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 50.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 11 ga wata ne, wasu kabilun yankin guda biyu suka gwabza fada kan dabbobi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 47 kawo yanzu. Shaidu sun bayyana a wata hira ta wayar tarho da wakilan kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, har yanzu ana ci gaba da gwabza fada da makami, kuma mazauna birnin Nyala na tserewa. Galibin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin samun kulawar jami’an lafiya.

Bugu da kari, ko da a jiya ma, sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, sun ci gaba da gwabzawa a Nyala da Khartoum, babban birnin kasar. (Ibrahim Yaya)