logo

HAUSA

Za a fara aikin binciko adadin filayen kiwo da gwamnati ta samar sama da shekaru 50 da suka gabata a jihar Gombe

2023-08-14 09:11:50 CMG HAUSA

 

Gwamnatin jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai gudanar da aikin tantance adadin filayen kiwo, gandun daji da burtalai da gwamnati ta kebe sama da shekaru 50 da suka gabata a jihar.

A lokacin da ya kaddamar da kwamitin, gwmanan jihar ta Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a binciko irin wadannan filaye domin bunkasa sha’anin kiwon dabbobi da kuma kawo karshen matsalolin rikicin Fulani da makiyaya a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.