logo

HAUSA

Duniya Ba Ta Bukatar Wani Sabon “Yakin Mummuke”

2023-08-14 19:13:31 CMG Hausa

Tun lokacin da gwamnatin Joe Biden ya fitar da rahoton dabarun tsaro na kasa a watan Oktoba 2022, Amurka ta shirya tsauraran matakai don mummuke kasar Sin. Gabar da take yi da kasar Sin na dada ta’azzara, ciki har da rikicin fasaha na baya-bayan nan wanda ake kira “Chip war”. Wannan matakin da Amurka ta dauka na nuni da sabon “Yakin cacar baki". Wanda fadar Washington ta kaddamar ba tare da shawarar kowa ba. Kuma wannan mataki ya sabawa yadda zamani ke tafiya a yanzu.

Al’umman Amurka na fama da mabanbanta matsaloli a cikin ’yan shekarun nan, musamman tabarbarewar tsarin siyasarta, tsadar rayuwa, korafe-korafe daga al’umma da rashin jituwa tsakanin jam’iyyun siyasar kasar, wadanda su ne ainihin tushen matsaloli da ya kamata ta magance. A maimakon haka, suke ƙoƙarin canza matsin lambar cikin gida da kasar ke fuskanta ta hanyar zuzuta abin da suke kira “barazana daga waje” wato kasar Sin.

A zahiri kuma, ’yan kasuwan Amurka sun nuna rashin amincewarsu a aikace yadda Amurka ke tafiyar da lamarin. Misali, tun farkon wannan shekara, sashe daga cikin shugabannin shahararrun kamfanoni suke dafifi zuwa kasar Sin don bincika damar hadin gwiwa. Bari mu fara da Starbucks, Sabon Shugaban kamfanin na kasa da kasa Laxman Narasimhan ya shaida girman damar dake akwai a kasuwar Sin. Shugaban Tesla Elon Musk ya bayyana a fili rashin amincewarsa da wannan lakabin da kasashen yamma suka yi wa Sin na “hadari” tare da yanke mu’amala da ita. Shugaban Nvidia Jensen ya ce ba su shirya “raba gari da Sin” saboda ba su da ikon yin haka, kuma kasancewar kasar Sin daya ce tak a duniya. Duk wadannan na nuni da irin muhimmancin kasuwar Sin game da kamanta adalci da tabbatar da moriyar juna.

Amma ga mutanen Amurkawa, ko da yake yankin Sin da Amurka suna da tazara da juna, akwai dadadden musayar zumunta tsakanin kasashen biyu mai dogon tarihi. Labaru da dama sun kara jadadda wannan matsayi: labarin damisa masu tashi wato “flying Tigers” a lokacin Yaƙin Duniya na II, labarin  "Guling Friends" a lardin Fujian dake gabashin Sin da kuma abota tsakanin Sin da Amurka ta “house in Muscatine” a jihar Iowa, da dai sauransu.

Tun lokacin barkewar rikicin Ukraine, kasashen Turai suka bi bayan ƙaddamar da takunkumai mabanbanta a kan Rasha, wanda ya koma kansu ya kuma karfafa rikicin makamashi da hauhawar farashin kayayyakin kasashensu. Tun daga wannan lokaci ne kasashen yamma suka fara nazari kan dangantakarsu da kasar Sin. Kwanan baya, shugaban kasar Faransa Emmanuel Mackron ya bayyana adawarsa game da shishigin Nato a yankin Asiya-Pacific. Kasashe Membobin Tarayyar Turai kamar Jamus, Hungary da Serbia sun bayyana a fili cewa ba za su "daina mu’amala" da Sin ba.

Muhimmin dalilin takun-saka tsakanin Amurka da Sin yana ta’allaka ne da irin tsarin manufofin Amurka a kan sauran kasashen duniya, wanda yake haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen guda biyu. Ita kasar Sin ta fahimci alfanun dake cikin samun nasara tare, a yayin da ita kuma Amurka ta gwammace ta yi babakere.

"Duniya tana da girman da za ta dauki ci gaban kowace kasa ba tare da wani ya nuna fifiko ba." Yayin zantawarsa da sakatare Tony Blinken na gwamnatin Amurka a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinpingy a ce, Sin da Amurka na iya yin hadin gwiwa don samun nasarorin da za su amfanar da daukacin duniya. Hadin gwiwa tsakanin ƙasashen guda biyu masu mafi girman tattalin arzikin duniya zai daidaita zaman lafiyar duniya, tare da ba da gudunmawa ga raya lamurra da  manufofin kasashe masu tasowa.  

Akwai dalilai da dama da za su sanya manyan giwaye biyu su yi zaman jituwa a cikin daji don bunkasuwa jejin da sauran dabbobin dake cikin shi. Ya kamata Amurka ta daina kumfar baki a kan abubuwan da ba su shafe ta ba. Misalin wannan shi ne sakon da ta aike tarayyar Najeriya a makon da ya gabata inda ta bukaci shugabannin Najeriya su yi taka tsantsan da basussukan da take ciyowa daga kasar Sin. Ya kamata Amurka ta maida hankali a kan daidaita matsalolinta na cikin gida saboda a halin yanzu “Duniya ba ta bukatar wani yakin mummuke”. (Yahaya Babs)