logo

HAUSA

An raya ayyukan al’adu da yawon shakatawa a Xinjiang zuwa wani sabon matsayi

2023-08-14 22:22:14 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, a halin yanzu, muna cikin muhimmin lokacin yawon shakatawa a nan kasar Sin, sabo da hutun lokacin zafi. Kuma jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta kasance wurin da mutane suka fi zuwa yawon bude ido, sabo da kyakkyawan yanayin jihar. Cikin shekaru baya-bayan nan, ayyukan al’adu da yawon shakatawa sun samu bunkasuwa cikin sauri a Xinjiang, a kokarin janyo hankulan masu yawon shakatawa.