logo

HAUSA

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun sha alwashin gurfanar da hambararren shugaban kasar bisa laifin cin amanar kasa

2023-08-14 14:13:56 CMG HAUSA

 

Gwamnatin soja da suka yi juyin milki a Jamhuriyar Nijar ta sha alwashin gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum a gaban kuliya, bisa laifin cin amanar kasa, tare da yin kakkausar suka ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da kakabawa kasar takunkumi.

Mamba a rundunar ceton kasa (CNSP) Kanar Manjo Amadou Abdramane, ya bayyana cewa, za a gurfanar da Bazoum a gaban kuliya saboda cin amanar kasa da kuma kawo cikas ga tsaro cikin gida da wajen Nijar.

Kafofin watsa labaran cikin gida sun ruwaito cewa, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta kakabawa Nijar takunkumi sakamakon juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan, tare da amincewa da aikewa da dakarun kota-kwana don gaggauta maido da kundin tsarin mulki a jamhuriyar Nijar, amma ta ci gaba da dagewa wajen neman hanyar diflomasiyya don magance matsalar, yayin da jagororin juyin mulkin Nijar din suka yi tir da takunkumin da aka kakabawa kasar, a matsayin wanda ya saba ka'ida, rashin tausayi da wulakanci. (Ibrahim)